News
Jami’an Hukumar DSS Sun Afka Ofishin SERAP, Sa’o’i Bayan Kama Shugaban NLC Joe Ajaero
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jami’an Hukumar DSS sun afka wa ofishin ƙungiyar kare haƙƙi da sa-ido kan gwamnati, wato SERAP da safiyar Litinin.
SERAP ta yi sanarwa a shafin ta na X, wato Tiwita cewa, “SSS sun afko mana sun mamaye ofishin SERAP a Abuja, sun zo su na neman daraktocin ƙungiyar.”
Siyasar Uban Gida: Burin Kwankwaso Na Mulkar Kano Ta Ƙarƙashin Ƙasa A Karo Na Uku Na Dab Da Cika
“Tilas Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta umartar SSS su kawo ƙarshen cin zarafi, tsoratarwa da kai wa ƙungiyoyin hare haƙƙi hare-hare,” inji SERAP.
Babu hukumar tsaron da ta fito ta ce ita ce ta tura jami’an ta ofishin SERAP ɗin tsakanin ‘yan sanda da kuma SSS.
PREMIUM TIMES ta bada labarin cewa Jami’an SSS sun kama Ajaero, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago.
Jami’an Tsaron Farin Kaya na SSS sun kama Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na Ƙasa, Joe Ajaero.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai daban-daban sun tabbatar da kamun da aka yi masa a filin jirgin sama na Abuja da sanyin safiyar yau Litinin.
Ba a dai san takamaimen dalilin kamun ba, amma dai ana ganin ba ya rasa nasaba da zargin da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ke yi masa da hannu wajen ƙoƙarin tayar da fitina ta hanyar ta’addanci.
