Connect with us

News

Hukumar NiMet Ta Yi Gargaɗin Samun Tsawa Da Ruwan Sama Na Tsawon Kwana 3 A Najeriya

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama daga Laraba zuwa Juma’a a faɗin Najeriya.

Advertisement

 

A cewar bayanai kan yanayi da hukumar ta fitar ranra Talata, ta ce ana sa ran samun tsawa a wasu sassan jihohin Najeriya kamar  Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da kuma Kaduna ranar Laraba.

Advertisement

 

‘Yan Sanda 32 Ne Kawai Ke Tsare Kauyuka 200 A Katsina – Gwamnatin Katsina

NiMet ta ce za a kuma samu tsawa a wasu ɓangarorin jihohoin Najeriya kamar  Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da kuma Jigawa da rana da kuma yammaci.

Advertisement

 

“A arewa maso tsakiya, ana sa ran samun tsawa a Abuja, babban birnin tarayya, Nasarawa da kuma jihar Neja a ranar Laraban,” in ji NiMet.

Advertisement

 

Hukumar ta ƙara da cewa a yankin kudancin ƙasar ma za a fuskanci tsawa da ruwan sama a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ogun, Ondo, Lagos, Edo, Delta, Cross River, da kuma Akwa Ibom daga Laraba zuwa Juma’a.

Advertisement

 

NiMet ɗin ta ce za a samu iska mai karfi kafin saukar ruwan saman a yankuna da dama, inda ta ja hankalin jama’a cewa su ɗauki matakan kariya da hukumomi suka fitar domin kare kansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending