Connect with us

News

GOMBE: Kungiyar ASUU Ta Sanar Da Fara Yajin Aikin ‘Sai Baba Ta Gani

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta bayyana fara yajin aikin ‘sai baba ta gani’ a jami’ar jihar Gombe (GSU) saboda gaza cimma matsaya a kan batun walwalar ma’aikata da yanayin aiki.

Advertisement

Yayin da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, shugaban kungiyar ASUU reshen GSU, Dakta Suleiman Salihu Jauro, ya ce shiga yajin aikin ya zama wajibi saboda tabarbarewar al’amuran koyo da koyarwa a jami’ar.

Ambaliyar Ruwan : Nan Da Sati Biyu Zamu Tabbatar Da Kowa Ya Koma Muhallinsa _ Kashim Shattima

Shugaban ya bayyana cewa sun shafe shekaru da dama suna kokari tare da bin hanyoyin warware matsalolin ta hanyar tattaunawa amma abin ya ci tura.

Advertisement

“Daga cikin manyan dalilan shiga yajin aiki akwai batun gazawar gwamnatin jiha wajen aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar ASUU a shekarar 2021 da bukatar neman kara yawan kudin da ake bawa jami’a da kuma biyan kudin alawus din koyarwa (EAA) na tsawon lokaci.

“Akwai wani bangare mai muhimmanci a yarjejeniyar da muka kulla da gwamnati a shekarar 2021, shine batun bawa jami’a kudin da yawansu ya kai miliyan N50 duk shekara, wanda har yanzu, bayan kusan shekara hudu har yanzu ko sisi basu taba bayarwa da sunan hakan ba,” a cewar Dakta Jauro.

Advertisement

Dakta Jauro ya kara da cewa rashin biyan Malaman jami’ar alawus din EAA na tsawon shekara biyar ya saka su a cikin mawuyacin hali tare da kassara kwazonsu na aiki.

Shugaban ya bayyana cewa rashin girmama yarjejeniyar daga bangaren gwamnati ya barsu da rashin wani zabi face su tsunduna yajin aiki tunda basu da wata sauran mafita kamar yanda jaridar WIKKI TIMES  ta ruwaito

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending