News
DA DUMI DUMI : Gwamnatin Jihar Kano Ta Sauya Ranakun Komawa Makarantu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano ta sake sauya ranakun komawa makarantun firamari da sakandire zuwa ranar Talata 17 ga Satumba, 2024.
A Yayin da daliban makarantun kwana a fadin jihar za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.
Cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, ta ruwaito cewa kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa sauya ranar komawa makarantun tana da nasa da yadda gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 16 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar hutu domin bikin Mauludi.
Saboda haka an sauya ranar ne domin baiwa dalibai damar gudanar da bukukuwan maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) wacce Kuma ta kasance Ranar litinin.
“A yayin da nake taya al’ummar Musulmi murna, ina kira gare su da su rungumi dabi’ar hakuri, sadaukarwa, da kishin kasa tare da ci gaba da yi wa jihar kano addu’a da kasa baki daya,” inji shi.
Don haka sanarwar ta bukaci iyaye da dalibai da su lura da sabuwar ranar da za a ci gaba da aiki don tabbatar da daliban sun koma makarantunsu kamar yadda aka sanya.
Nigerian Tracker
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
