News
Shugaba Tinubu ya saka hannu kan kudirin kafa cibiyar hana yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba –NSA
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya rattaba hannu kan kudurin dokar kafa cibiyar kula da kananan makamai ta kasa.
Ribadu ya bayyana haka ne a wajen taron karawa juna sani kan hana yaduwar kananan makamai a Najeriya da kuma yankin yammacin Afirka a ranar Talata a Abuja.
Banbancin Da Ke Tsakanin Muhammad Bello Matawalle Da Gwamna Dauda Lawal —Daga Imam Murtadha Gusau
Ya ce hakan zai ƙara wa cibiyar kwarin guiwa wajen gudanar da ayyukanta.
A jawabinsa na bude taron, kodinetan hukumar NCCSALW na kasa DIG Johnson Kokumo mai ritaya, ya ce cibiyar a ‘yan kwanakin nan, ta samu wasu muhimman nasarori a yaki da yaduwar kananan makamai ba bisa ka’ida ba.
Kokumo ya ce, a ranar 1 ga watan Yuli, cibiyar ta kwato wasu tarin haramtattun makamai daga hukumar kwastam ta Najeriya, daga bisani kuma ta kama wasu mutane 10 da ake zargi da hannu wajen shigo da su ba bisa ka’ida ba.
Ya ce a halin yanzu hukumar NCCSALW tana tuhumar wadanda ake zargi da shigo da su Najeriya ba bisa ka’ida ba, da kayayyakin da aka haramta – Bindigogi 544 da harsasai 112,500 wanda ya sabawa sashe na 3 (6) na Dokar Laifukan Mabambantan Cap M17 na Tarayyar Najeriya 2004 da dai sauransu.
Cibiyar Yaki da Kananan Makamai ta Kasa (NCCSALW) ce ta shirya taron bitar.
Darakta Ibrahim Babani ne ya wakilci Ribaɗu a wurin taron.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
