News
CITAD Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Kafafan Sada Zamunta Karo Na Biyar Kan Fasahar AI
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce Artificial Intelligence AI na da gagarumar gudammawa wajaninganta ayyukan jama’a, da sake fasalin harkokin zabe a Najeriya.
Gwamna Abba ya bayyana haka ne wajan horo na musamman yadda za’a habbaka tasirin aikin jarida a kafafan Sada zamunta da kuma kasuwanci Zamani a yanar gizo wanda duk shekara cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD Ta shirya.
Warware Zare Da Abawa Tsakanin Kamfanin NNPCL Da Matatar Dangote A Kan Farashin Man Fetur
Wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa na musamman kan al’amuran Jiha Usman Bala, ya bayyana cewa, Fasahar Artificial Intelligence AI na da karfin daidaita tsarin zabe, da rage kurakuran dan Adam.
“Bayar da abubuwan da suka faru a babban zaben Najeriya na 2023 wanda ya shaida yadda ake amfani da matasa masu rauni wajan tashe-tashen hankulan zabe da kuma cin hanci da rashawa na jami’an zabe”
Ya ce bayyanar AI ya a ba da damar da za ta iya magance yawancin matsalolin tsarin da suka shafi tsarin zaben Najeriya a tarihi.
Babban Darakta, cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma( CITAD) Injiniya Yunusa Ya’u ya jaddada cewa, taron na da nufin yin nazari kan tasirin da kuma amfani da damar fasahar AI.
“Mun yi babban zabe a bara kuma mun sami tambayoyi da yawa kuma muna tunanin tare da AI yawancin waɗannan tambayoyin za a amsa.
