Connect with us

News

Ƴan Najeriya Na Jiran Sakamakon Binciken Da Aka Gudanar Kan Seaman Abbas

Published

on

9b8dd982 67f0 4fa8 bd5d 76b826e2aa41 cx0 cy1 cw0 w408 r1 s

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Yan Najeriya suna ta zazzafar mahawara shafukan sada zumunta game da zargin cin zarafi da kuma azabtar da wani sojan ruwa bayan da matarsa ta bayyana cewa an ɗaure shi tsawon shekara shida cikin mummunar yanayi har ya samu taɓin hankali.

Advertisement

Sojan ruwan mai suna Abbas Haruna da Matarsa  mai suna Hussaina ta bayyana cikin wani faifen bidiyo da tayi hira da gidan rediyon Berekete a Abuja cewa an gana masa uƙubar da ta wuce misali.

‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Tsadar Iskar Gas

Matar ta bayyana wasu zarge-zargen cewa ba a yi wa mijinta da ma su iyalansa ɗin adalci ba.

Advertisement

Hussaina, ta bayyana cewa mijin nata ya samu saɓani ne da wani babban hafsan soja, inda tun a lokacin aka kama shi, aka tsare, kuma a cewarta kusan shekara shida ke nan yana tsare.

Bidiyon na Hussaina ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka riƙa yaɗa shi, wasu na zagi, wasu na Allah wadai, wasu kuma suna cewa a dai yi bincike.

Advertisement

Babban abin da ya ja hankalin mutane shi ne yadda Hussaina ta bayyana yadda ta sha faɗi-tashi da tafiye-tafiye tsakanin Kaduna da Taraba da Abuja da Gombe duk a kan mijin.

 

Advertisement

 

Daily News24

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending