Connect with us

News

Yunwa Ba Hujja Ba Ce Da Mutum Zai Sayar Da Ƙuri’ar Sa Ranar Zaɓe’ – Sanata Oshiomhole

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa ba daidai, ko hujja ko dalili ba ne da wasu mutane za su ce wai yunwa ce ke sa su sayar da ƙuri’in su, domin su ci abinci.

Advertisement

Oshiomhole, wanda a yanzu sanata ne daga Jihar Edo, ya bayyana haka a lokacin da ya je jefa ƙuri’a a mazaɓar sa, a zaɓen yau Asabar.

Ƴan Najeriya Na Jiran Sakamakon Binciken Da Aka Gudanar Kan Seaman Abbas

Ya ce ya kamata idan mutum zai aikata laifi ko ba daidai ba, to ya daina kafa hujja da matsalar rayuwa, ko taɓarɓarewar tattalin arziki.

Advertisement

Oshiomhole ya ce duk waɗanda jami’an tsaro suka kama su na sayen ƙuri’u ko wani laifi, ‘yan PDP ne waɗanda dama sun sha alwashin za su tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓe.

 

Advertisement

Premium Times

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending