News
Kotu Ta ce Za A Fara Kama Masu Kera Muggan Makamai Da Sayar Da Su Ga ‘Yan Daba A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotu Shariar Musulunci da ke Fagge ta ce za a fara kama masu kera muggan makamai da sayar da su ga ‘yan daba a jihar Kano
Bayanin haka na kunshe cikin wani Sako da Barista Abba Hikima ya wallafa a Shafinsa na Facebook kamar haka:
Yunwa Ba Hujja Ba Ce Da Mutum Zai Sayar Da Ƙuri’ar Sa Ranar Zaɓe’ – Sanata Oshiomhole
“Alkalin Kotun Shariar Musulunci ta Fagge, Hon Umar Lawan Abubakar, ya umarci yan sandan Jihar Kano, daga kan AIG, Kwamishina da dukkannin DPOs da su tabbata duk lokacin da aka kama yan daba masu dauke da muggan makamai, su binciko masu kera waɗannan makamai da sayar da su ba tare da kaidi ba domin haɗawa da su a cikin tuhuma.
Kari akan wannan hoɓɓasa daga ɓangaren sharia, akwai buƙatar yin doka a jihohi aka wannan gaba. Domin wasu makaman da ake ƙerawa ake siyarwa waɗannan ƴan daba, suna taimakawa wajen ƴaɗa dabanci.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
