News
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Biyan N77,000 A Matsayin Alawus Ga ‘Yan Yiwa Kasa Hidima NYSC
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Tarayya ta amince da karin alawus na ‘yan yiwa kasa hidima wato NYSC zuwa Naira Dubu Sab’in da Bakwai (N77,000) a kowane wata, wanda zai fara aiki daga watan Yuli na 2024.
Wannan na da alaka da dokar albashi mafi karanci ta kasa da aka gyara (National Minimum Wage Amendment Act 2024).
NYSC ta bayyana hakan a shafinta na Facebook a daren Laraba.
Ta kara da cewa amincewar tana cikin wata takarda daga Hukumar Kula da Albashi da Alawus ta Kasa, wanda aka rubuta a ranar 25 ga watan Satumba 2024, kuma Shugaban hukumar, Mista Ekpo Nta, ya sanyawa hannu.
Kafin wannan, Babban Darakta na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed, ya kai ziyara ga Shugaban hukumar inda ya bukaci samar da kyakkyawan shirin jin dadi ga ‘yan yiwa kasa hidima NYSC.
Shugaban hukumar NYSC ya yi godiya ga Gwamnatin Tarayya bisa wannan tallafi akan lokaci, kuma yana da kyakkyawan fata cewa wannan zai kawo sauki ga ‘yan yiwa kasa hidima tare da kara musu kwarin gwiwa da kuma zaburar da su wajen yin aiki tukuru don ci gaban kasa.
Kafin wannan kari, ana biyan ‘yan yiwa kasa hidima alawus din naira Dubu Talatin da Uku (N33,000) a kowane wata.
