News
Zaben Kananan Hukumomi: Ba Abinda Rashin ‘Yan Sanda Zai Haifar —Gwamnan Ribas
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya bayyana mamakinsa game da zargin ‘yan sanda da yunkurin mamaye harabar hukumar zaben jihar (RSIEC) da nufin kawo cikas ga zaben kananan hukumomin da ake shirin gudanarwa a yau Asabar kamar yanda Muryar Amurka ta ruwaito
A jawabinsa yayin wani taron manema labarai a fadarsa dake birnin Fatakwal a yau Juma’a, gwamna Fubara yace yunkurin yazo da mamaki kasancewar ya samu labari a baya dake nuna cewar ‘yan sanda na niyar janyewa daga zaben kananan hukumomin.
Shugaba Tinubu ya bai wa Kakakin Majalisa Tajudeen lambar girma ta GCON
Ya kuma yi tambayar ko mene ne dalilin da ya sa jihar Ribas ta fita daban, musamman abinda ya bayyana da sa ido mara tushe a kan hukumar zaben dake karkashin hurumin jiha.
Ya kara da cewar hukuncin kotun Abuja ya umaurci ‘yan sanda ne kawai da kada su samar da tsaro, amma ba wai su mamaye harabar hukumar zabe ta jihar ribas (RSIEC) ko kuma yin katsalandan a zaben ba.
A cewar gwamna Fubara, kamata yayi a baiwa hukuncin babbar kotun jihar Ribas fifiko, kasancewar shi aka fara bayarwa.
