News
Gwamnatin Tarayya Ta Amincewa Dillalan Man Fetur Sun Fara Dauko Man Fetur Kai Tsaye Daga Matatar Dangote angote
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya ta bai wa ‘yan kasuwar man fetur izinin fara dauko mai kai tsaye daga matatar dangote ba tare da bin ta hannun Kamfanin Man Fetur na kasa, NNPCL ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ministan kudi kuma shugaban kwamitin aiwatar da siyar da danyen mai ta hanyar amfani da kudin Naira, Wale Edun ya sanyawa hannu, domin karin haske kan yadda aka fara sayan danyen mai da kuma sayar da kayayyaki da kudin Naira.
A Daina Tunanin Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Sake Manufofinta —Jam’iyyar APC
Kwamitin da Edun ke jagoranta ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki na biyu bayan fara aiki a ranar 10 ga watan Oktoba, domin tantance irin ci gaban da aka samu a shirin sayar da danyen mai da tataccen mai da kudin na Naira.
Sanarwar ta ce “masu kasuwancin albarkatun man fetur yanzu suna iya siyan man kai tsaye daga matatun mai na cikin gida ba tare da bi ta hannun kamfanin NNPC ba. ‘muna karfafa gwiwar dillalan man da su yi sayayya kai tsaye daga matatun mai bisa sharudan kasuwanci da aka kulla, wanda zai inganta kasar da kuma kasuwanci,”
Edun ya kuma ci alwashin cewa, nan da wani dan lokaci, matakan da aka dauka za su samar da ingantaccen yanayin kasuwanci don amfanin dukkan ‘yan Najeriya.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
