Connect with us

News

An Kama Ɗan Shekara 18 Bisa Zargin Sa Da Laifin Yin Garkuwa Da Ɗan Shekara Biyu

Published

on

An kama ɗan shekara 18 bisa zargin sace ɗan maƙota a Sakkwato

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Rundunar ƴan sanda ta yi nassarar  kama wani matashi mai suna Abba Aliyu da ake  zargi da laifin yin garkuwa da wani ɗan ƙaramin yaro jihar sokoto.

Advertisement

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da  Kakakin rundunar yan sandan, ASP Ahmed Rufa’i ya futar, ya ce sun samu ƙara ne daga wani Ibrahim Shehu a ranar 16 ga watan Oktoba kan cewa ɗansa da mai kimanin shekaru biyu ya ɓata tun a ranar 13 ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 6 na yamma.

‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Daliban JSS 3 Guda Biyu Bisa Zargin Satar Wayoyi 100 

An yi ta ƙoƙarin gano inda yaro ya ke, amma hakan bai sa an yi nasara ba har sai da wanda ya yi garkuwa da shi ya nemi a biya Naira miliyan biyu a matsayin kuɗin fansa wanda daga bisani aka biya N500,000 kafin aka sako yaron.

Advertisement

Daga nan ne jami’an suka yi nasarar kama shi bayan gudanar da binciken sirri a yankin Badon Hanya inda nan ne matashin ya ke da zama.

A lokacin da ake gudanar da bincike game da lamarin, matashin ya amsa laifinsa inda ya ce ya yi hakan ne don ya samu kuɗi daga iyayen yaron.

Advertisement

 

 

Advertisement

BLUEPRINT

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending