Connect with us

News

TIRKASHI: Wani Mahaifi Ya Dana Wa ’Yarsa Budurwa Kyamarar CCTV A Kai Don Sa Mata Ido

Published

on

TIRKASHI Wani Mahaifi Ya Dana Wa ’Yarsa Budurwa Kyamarar CCTV A Kai Don Sa Mata Ido

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Wani faifan bidiyo ya bazu a kwanan nan wanda ke nuna wata hanya mai ban mamaki da wani mahaifi ya dana wa ’yarsa Budurwa Kyamarar CCTV a kai don sa mata ido kan abinda ka je ya zo a kasar Pakistan.

Advertisement

Wannan bidiyon ya jawo hankalin jama’a a tsakanin masu amfani da yanar gizo.

A cikin faifan bidiyon, ana iya ganin yadda Budurwa ta yi hira da wani mutum kuma akwai wata babbar kyamarar CCTV da aka dora mata a kai.

Advertisement

Da aka tambaye ta game da hakan, ta ce ra’ayin mahaifinta ne, inda ta kara da cewa ba ta da wani abin cewa game da kyamarar kanta saboda ta san iyayenta sun damu da kulawa da lafiyarta.

Budurwar da a aka sakaya sunanta, ta ci gaba da cewa, tunanin saka na’urar da ake zaton na’urar ɗaukar hoto ce mai amfani da batir a lokacin da za ta fita, ya samo asali ne daga mutuwar wata budurwa a garin Karachi.

Advertisement

Mahaifinta, wanda ta kira da “mai ku;a da lafiyarta duk inda take,” da alama ya gaya mata cewa kyamarar sa-ido za ta taimaka masa ya kula da ita sosai, kuma ta yarda ta ɗaura kyamarar.

Duk da matakin da ake kira matakin tsaro, yarinyar ta yi ikirarin cewa barazanar cin zarafin mata a Karachi gaskiya ce, kuma iyayenta suna da cikakken dalilin damuwa.

Advertisement

Ba a dai bayyana yadda ake amfani da kyamarar sa ido ba da kuma yadda sakon zai iya kaiwa ga mahaifin matar, amma shafukan sada zumunta sun nuna cewa, kyamarar ba za ta yi amfani sosai ba, idan wani ya kai wa yarinyar hari ta baya. Haka kuma, watakila iyayenta suna dogara ga cewa ganin kyamarar tsaron zai tsoratar da duk wanda ke da mummunan nufi kan ’yarsu.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

TIMES OF INDIA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending