Connect with us

News

Babban Hafsan Sojoji Janar Lagbaja Na Nan Da Ransa – Rundunar Sojin Najeriya

Published

on

Janar Lagbaja na nan da ransa – Rundunar Sojin Najeriya

DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da rade-radin mutuwar babban hafsan sojin kasa (COAS), Taoreed Lagbaja, da wasu mutane suka yi a dandalin sada zumunta.

Advertisement

Sojojin sun karyata jita-jitar a wani sako da suka wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, inda suka yiwa wani rubutun Jackson Ude lakabi da “Labarin Karya”.

TIRKASHI: Wani Mahaifi Ya Dana Wa ’Yarsa Budurwa Kyamarar CCTV A Kai Don Sa Mata Ido

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wasu rahotanni na yanar gizo sun yi hasashen cewa Lagbaja, Laftanar Janar, ya rasu ne a wani asibiti da ba a bayyana ba a kasar waje.

Advertisement

Dukkanin rahotannin sun ambato Jackson Ude a matsayin majiyarsu ba tare da wani tabbaci a hukumance daga hedkwatar sojoji da tsaro ba.

Sai dai Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, a ranar Asabar, ya ba da sanarwar cewa COAS na hutu tare da kula da lafiyarsa a wajen kasar.

Advertisement

Bayan haka Nwachuku ya ce ba abar wannan ofis babu kowa ba, Manjo Janar, Abdussalam Ibrahim, na rike da ofishin kafin Lagbaja ya dawo daga hutu.

” Komai da ake yi a aikin soja a tsare yake. Ba za a bar wannan sakatete ba babu wani da zai zauna a madadin babbana hafsan sojojin kasan ba.

Advertisement

Ya yi kira da mutane da su yi watsi da wannan jita-jita, yana mai cewa Lagbaja na nan a kuma ana sa ran dawowarsa idan ya kammala hutun sa da duba lafiyarsa.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending