News
Gobe Raudhatur-Rasul za ta yi bikin shekaru 16 da Kafuwa a Kano
DAGA IBRAHIM HAMISU
Kungiyar Raudhatur-Rasul za ta yi bikini cika shekara 16 da kafawa, da karrama Zakarun gasar musabaka yabon ma’aiki S.A.W da kuma karrarama muhimman mutane, da zai gudana a gidan Mumbayya, ranar Lahadi da karfe 10:00 ba safe.
Bilyaminu Zakariyya da aka fi sani da Abul-warakat Ayagi, shi ne shugaban kungiyar ya bayyana cewa taron zai zama na musammam domin ya ce zaa baje-kolin tarihi da ayyukan da kungiyar ta yi shekaru 16, da kuma karbar shawarwarin inganta ta,
“Taro ne na godiya ga Allah, da a cikin huwacewarsa ya sa wannan kungiya ta cika shekaru 16 da kafawa, da tarin nasarori da ayyuka, wadanda muka kididdige nau’o’in ayyuka 38, da muka yi, wasu suka maimata, wasu sau uku, biyar, bakwai zuwa sama, muka kuma kididdige ayyuka 135 da muka yi cikin wannan shekaru.
“Abu na biyu da taron zai kunsa, akwai musabakar sha’iran jahar Kano da muka kirkira, domin tsaftace harshe da alkalami a yabon Annabi (S. A. W), a karo na farko mai martaba sarkin Kano ya halarta ya ba kyaututtuka fa zakarun, to yanzu karo na uku kenan, a taron za a karrama hazikan sha’iran da suka yi zarra. Abu na karshe, shi ne karrama muhimman mutane da suke tallafa kungiyar ko al’umma a mabanbantan bangarori”
Ya kara da cewa “Shi wannan taron sha-kundum ne, domin zai hadiye duk tarurrukanmu na baya,
“A da mukan yi taro a mataki unguwa, karamar hukuma da ma na jahar, amma wannan duk ya fi su girma, sannan akwai manyan mutane masu mabambantan mukamai, da malamai da shehunnai da sha’irai da manyan ‘yan siyasa da kuma ma’aikata” inji Abul-warakat Ayagi
