Connect with us

News

Gazawar Gwamnatin Tinubu A Bayyane Take Karara  —Obasanjo

Published

on

Ya kamata shugabannin Nijeriya da yawa su kasance a gidan yari Obasanjo

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi kakkausar suka ga halin da Najeriya ke ciki a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, tabbace kuma a bayyane yake nunawa kuma ya bayyana don kowane mai gaskiya ya gani.

Advertisement

Bayanin hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai taimaka wa Obasanjo kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, ya saki ranar Asabar.

Gobe Raudhatur-Rasul za ta yi bikin shekaru 16 da Kafuwa a Kano 

Haka zalika ya bayyana Tinubu a matsayin “Baba-go-slow”, ya kuma dora alhakin tabarbarewar al’amuran Najeriya da suka hada da cin hanci da rashawa, tabarbarewar tattalin arziki, da rashin tsaro.

Advertisement

Obasanjo ya alakanta rikicin kasar da gazawar shugabanci, yana mai cewa matsalar ba ta al’umma ba ce ko kuma dukiyar kasa, sai dai rashin iya shugabanni.

Ya kara da cewa manyan masu fada a ji suke amfani da dukiyar jama’a don amfanin kansu, al’adar da ya yi imanin ta zama ruwan dare a karkashin Gwamnatin Shugaba Tinubu.

Advertisement

A cewar Obasanjo, wannan nau’i na cin hanci da rashawa ya haifar da sayar da kadarorin kasa da kuma tabarbarewar ayyukan gwamnati da suka hada da ilimi da kuma kiwon lafiya, wanda a karshe ke kawo cikas ga ci gaban Najeriya.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda ake tafiyar da tattalin arzikin kasar, inda ya yi gargadin cewa ana kara yin shawarwari ne bisa muradun wasu masu karfi maimakon amfanin jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending