Connect with us

Business

Farashin Man Fetur A Matatar Fatakwal Ya Fi Tsada Akan Na Matatar Dangote Da Naira 75

Published

on

Matatar Man Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gazawa wurin gudanar da ayyukanta

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kungiyar Petroleum Products Retail Outlets Owners Association of Nigeria (PETROAN) ta bayyana cewa farashin man Fetur na matatar mai ta Fatakwal ke samarwa ya fi tsada idan aka kwatanta da wanda matatar mai ta Dangote ke samarwa.

Advertisement

Mai magana da yawun kungiyar, Dr. Joseph Obele, ya bayyana hakan a lokacin bikin sake bude matatar mai ta Fatakwal, wacce yanzu tana aiki da ƙarfin fitar da ganga 60,000 na mai a kullum.

YANZU-YANZU: Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Yahya Bello gaban kotu a abuja kan zargin wawushe Naira Biliyan 80

Ya ce farashin Man Fetur daga tsohuwar matatar mai ta Fatakwal ya fi wanda matatar Dangote ke siyarwa da naira 75 kowace lita.

Advertisement

Ya bayyana cewa matatar Dangote na siyar da litar man Fetur ga ‘yan kasuwa akan N970, yayin da farashin NNPCL yake tsaye akan N1045, bambancin da ke kai N75 kowace lita.

Ya kara da cewa wannan bambancin farashin na N75 babban ƙalubale ne ga ‘yan kasuwa, musamman a masana’antar da ribar kasuwanci take dogara ne da araha da gasa mai kyau.

Advertisement

 

 

Advertisement

SHAHARA REPORTS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending