News
Yadda Jami’oi Masu Zaman Kansu Ke Rabon First Class Ga Dalibansu, Gaskiya Akwai Lauje Cikin Nadi —Kungiyar ASUU
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Shugaban Kungiyar Malaman Jami’oi ta Najeriya (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya soki tsarin da jami’oi masu zaman kansu ke amfani da shi wajen bai wa dalibansu takardar shaidar kammala digiri a matakin mai daraja ta daya wato( First Class).
Ya ce sam lamarin ya zama tatsuniya ya kuma zama shiririta, matukar Jami’oi masu zaman kansu za su rika fifita samun kudi kan ingantaccen ilimi to kuwa hakan zai ci gaba da janyo koma baya da harkar ilimi a Najeriya
Osodeke ya ce idan jami’o’in gwamnati suka rungumi irin wannan dabi’a ba tare da ka’ida ba, hakan na iya haifar da koma baya a faggen ilimi na gaske.
A cewarsa, makarantun firamare da sakandire a halin yanzu suna samar da daliban da suka kammala karatun mai inganci da karancin ilimi.
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
-
News3 days ago
Uba Ya Nemi Kotu Ta Tilasta Wa ’Yarsa Ta Fitar Da Mijin Aure A Kaduna
