News
An Yanke Wutar Lantarkin Jami’ar ABU Saboda Gaza Biyan Kudin Wuta
An yanke wutar lantarkin Jami’ar ABU Zariya saboda gaza biyan kudin wuta
Wata sanarwa da Hukumar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta fitar, ta bayyana cewa ma’aikatan lantarki na Jihar Kaduna sun katse layin lantarkin da ya kai wa jami’ar wuta.
Gwamnatin Kano Ta Dawowa Da Jami’ar Northwest Sunanta Na Asali
Sanarwar ta ce hakan na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya akan kuɗin wutar da jami’ar ke sha a kowane wata, duk da cewa jami’ar ta yi iƙirarin biyan kuɗin wuta na sama da Naira biliyan ɗaya a wannan shekarar.
A baya-bayan nan ne dai aka bayyana Jami’ar ABU a matsayin jami’ar da ta fi kowace jami’ar gwamnati fice a Najeriya.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
