News
Zargin Rashawa : Kotu Ta Tura Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello Gidan Yari
DAGA UMAR ABDULLAHI HOTORO
Kotun tarayya da ke zamanta a Maitama ta ƙi amincewa da belin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nema, inda ta bayar da umarnin a ajiye shi a gidan yarin Kuje.
Mai shari’a Maryann Anineh ta ce an yi gaggawar neman belin Yahya Bello kamar yadda ta bayyana a zaman kotuna.
Yahaya Bello da wasu masu muta ne Biyu wanda suka hadar da Abdulsalami da Umar Oricha ne suke fuskantar tuhuma kan zargin almundahanar kuɗi naira biliyan 110.4.
Hukumar EFCC ce ta yi ƙarar Yahaya Bello da sauran mutanen kan tuhume-tuhume 16 da suka haɗa cin amana da almundahana kudaden Al’umma.
Sai dai kotun ta bayar da belin sauran waɗanda ake zargi tare da gindayamusu sharadai da wadan suka amshi belinsu.
Daga karshe kotun ta bukaci a cigaba da tsare Yahya Bello har sai lokacin da aka cike ka’idojon beli.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
