Connect with us

News

Kasar Saudiyya Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Mutum 6 Masu Fataucin Kwayoyi

Published

on

Rataya

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu Iraniyawa 6 saboda fataucin kwayoyi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (SPA) ta sanar a yau Laraba.

Advertisement

An zartarwa Iraniyawan hukuncin kisan ne a yankin Dammam dake gabar tekun Fasha na masarautar, saboda samunsu da laifin fataucin ganyen tabar wiwi cikin Saudiyya, kamar yadda ma’aikatar cikin gidan kasar ta bayyana a sanarwar da SPA ya wallafa ba tare da fayyace hakikanin ranar da aka zartar da hukuncin ba.

Ana Zargin Wani Babban Jami’an Hukumar REMASAB Da “Wawure” Kuɗaɗe A Kano

Mahukuntan birnin Riyadh sun zartar da hukuncin kisa a kan mutane 117 a 2024 saboda fataucin kwayoyi, a cewar alkaluman hukumar da kamfanin dillancin labaran AFP ya wallafa

Advertisement

A 2023, hukumomin Saudiyya sun kaddamar da gangamin yaki da kwayoyi da aka yi matukar yayatawa da ya sabbaba dimbin samame da kame

 

Advertisement

VOA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending