Connect with us

News

An Kone Adaidaita Sahun Barayin Waya a Kano 

Published

on

An kone babur din barayin waya a titin Ibrahim Tai

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Wasu fusatattun matasa sun kona wata Adaidaita Sahun, da ake kyautata zaton na masu satar waya ne akan titin Ibrahim Taiwo dake  birnin Kano.

Advertisement

Bayan kone baburin an kuma yi nasarar kama masu babur din tare da mika su hannun jami’an tsaro.

Mutane Saba’in Da Bakwai Sun Rasa Rayukansu A Ya Yin Fashewar Tankar Mai A Neja 

Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan ya ce wadanda ake zargin suna hannun jami’an tsaro.

Advertisement

Kiyawa, yace an samu waya guda biyar a wajen su.

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Lamarin dai ya faru a daren yau asabar.

Advertisement

Satar waya a wajen wasu daga cikin masu Adaidaita Sahun ta zama ruwan dare a wasu sannan jihar Kano.

wanda irin haka ta faru kwanakin baya a kofar shiga asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, da aka samu wasu masu sace waya a babur inda aka kone musu babur din suma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending