News
Kashi 9.6 Na Daliban Primary A Kano Ne Kawai Suke Da Kwarancewar Karatu —UNICEF
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF), ya ce, daliban makarantun Primary kaso 9.6 ne kacal suke da kwarancewar karatu a jihar Kano.
Babbar jami’ar asusun na UNICEF a Kano, Rahama Muhammed ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Kano a wani bangare na bikin ranar ilimin boko na duniya.
Kotu Ta Garƙame Matar Da Ke Yin Leken Asiri A Sakonnin Whatsapp Na Mijinta
Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce kashi 9.6 cikin 100 kawai na daliban makarantaun firamare a jihar Kano suka iya karatu, yayin da kashi 11.2 cikin 100 su ka iya lissafi s matakin farko.
Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Mohammed ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kan bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025, a jiya Juma’a a Kano.
A cewarsa, jihar na fama da matsananciyar matsalar ilimi, inda kimanin yara miliyan ɗaya ke kasancewa ba sa zuwa makaranta, bisa ga bayanan da aka samu daga rahoton 2021 na ‘Multiple Indicator Cluster Survey (MICS)’.
Ya kuma ce rahoton ya nuna cewa yara 989,234 masu shekarun makarantar firamare, wanda ya kai kusan kashi 32 cikin ɗari na al’umar jihar, ba sa halartar makarantu tun daga tushe a Kano.
Mohammed ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara maida hankali kan gyaran ilimi a jihar, musamman a matakin farko.
