News
Ɓarawo Ya Mutu Sakamakon Konewa Da Wutar Lantarki Yayin Da Ya Ke Kokarin Sata A Taransifoma
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Advertisements
Advertisements
Wani mutum da ba a kai ga gane sunan sa ba ya mutu sakamakon konewa da wutar lantarki yayin da ya ke kokarin sata a cikin taransifoma a yankin Akute, Jihar Ogun.
Advertisements
Jaridar DAILY NIGERIAN ta gano cewa al’ummar yankin suna fama da matsaloli na satar wayoyin lantarki da lalata injinan wutar su.
Advertisements
Advertisements
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, ta ce mamacin ya hau gidan injin wutar kuma yayin da yake kokarin yanke waya, wutar ta kashe shi.
Ta bayyana cewa jagoran al’ummar Irewole ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yansanda.
Advertisements
