Connect with us

News

Tallafin Naira Biliyan 150 Ne Yasa Gwamnan Kaduna Ke Goyon Bayan Tinubu — El-Rufa’i

Published

on

FB IMG 1738668006974

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya caccaki gwamnan jihar Kaduna mai ci, Sanata Uba Sani, kan yadda yake bayyana goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. El-Rufa’i ya bayyana cewa dalilin goyon bayan da Uba Sani ke nunawa ba komai ba ne illa son kai da bukatar samun tallafin Naira biliyan 150 daga gwamnatin tarayya.

Advertisement

Tsohon gwamnan ya bayyana wannan ra’ayi nasa ne a matsayin martani ga kalaman da Gwamna Uba Sani ya yi a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC. A cikin tattaunawar, Uba Sani ya nuna mamaki kan yadda wasu daga cikin mambobin da suka kafa jam’iyyar APC ke kalubalantar shugabancin Tinubu da manufofinsa.

Gwamnatin  Kano Za Ta Kafa Kwamiti Domin Bincike Kan Abinda Ya Faru A Rimin Zakara

A cikin bayanansa, Uba Sani ya bayyana cewa abin takaici ne yadda wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar ke nuna kin amincewa da manufofin Tinubu, duk da kasancewarsa shugaban kasa daga jam’iyyarsu.

Advertisement

Sai dai El-Rufa’i ya jaddada cewa goyon bayan da Uba Sani ke nunawa ga Tinubu ba ya da alaka da kishin kasa ko jam’iyya, illa neman cimma muradunsa na kashin kai, musamman ta fuskar neman tallafi daga gwamnatin tarayya don cike gibin tattalin arzikin jihar Kaduna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending