News
’Yan Uwan Juna Uku Sun Gurfana A Kotu Kan Dukan Miji Da Mata A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano, an gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gezawa kan zargin dukan wata mata da mijinta har sun ji munanan raunuka.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen ukun sun yi wa matar aure dukan kawo wuƙa, wanda ya haddasa fashewar ƙafarta da hannunta. Har ila yau, sun kuma farmaki mijinta wanda ya yi ƙoƙarin cetonta, inda shi ma suka jibge shi.
Majalisar Dokokin Kano Ta Bukaci Sake Duba Dokar Amfani da Ƙasa
A cewar tuhumar da ake musu, ana zarginsu da laifin yin kutse, barazana, haɗa kai wajen aikata laifi da kuma jikkata mutane.
A gaban kotu, duk waɗanda ake tuhuma sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a a yankin.
Kotun dai za ta yanke hukunci a kan lamarin nan ga
ba kadan.
