News
An Gano Ma’aikatan Bogi 2,363 Da Ke Karbar Albashin Naira Miliyan 193.6 A Zamfara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta gano ma’aikatan bogi 2,363 a yayin tantance ma’aikatan gwamnati da aka kammala kwanan nan.
Gwamna Dauda Lawal ne ya kafa kwamitin tantancewar a watan Agusta 2024, karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan jihar. A cewar Suleiman Idris, kakakin gwamnan, an gudanar da tantancewar ne domin tabbatar da shirin biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 a jihar.
Jami’an Hukumar NAFDAC Sun Rufe Manyan Kasuwannin Magunguna Uku
Sakamakon Tantancewar
Rahoton kwamitin ya bayyana cewa daga cikin ma’aikatan jihar, mutum 27,109 ne kawai aka tabbatar da sahihancinsu. Sai dai kuma an gano:
Ma’aikatan bogi 2,363 na karbar N193,642,097.19 duk wata ba tare da wata sahihiyar aiki ba.
Ma’aikata 1,082 da suka kai shekarun ritaya amma har yanzu suna karbar albashi na N80,542,298.26 a kowane wata.
Ma’aikatan kwangila 395 da mutum 261 da ba sa cikin rajistar ma’aikatan jihar.
Kananan yara 220 a cikin jerin ma’aikatan da ke karbar albashi, ciki har da 75 da aka dauka aiki ba tare da cika sharuddan shekarun daukar aiki ba.
Ma’aikata 12 da ke karbar albashi har N726,594 duk wata ba tare da kasancewa cikin rajistar ma’aikata ba.
Ma’aikata 207 da ba a tantance su ba, suna karbar N16,370,645.90 duk wata.
Matakan da Gwamnati Za Ta Dauka
Gwamnatin Zamfara ta ce za ta ci gaba da tantancewar domin tabbatar da gaskiya da adalci a gudanar da ayyukan gwamnati. Haka kuma, an sanya ranar fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 a watan Maris.
Kwamitin ya jaddada cewa kudaden da ake biyan ma’aikatan bogi na iya inganta rayuwar sahihan ma’aikatan gwamnati idan aka yi amfani da su yadda ya kamata.
