Connect with us

News

An Kashe Wani Jami’in Hukumar NDLEA Ta Hanyar Kona Shi Kurmus A Kaduna

Published

on

An kashe wani jami'in hukumar NDLEA ta hanyar kona shi kurmus a ji

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wasu ‘yan tarzoma a garin Gadar-Gayan da ke yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun kashe wani jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Aliyu Imran, ta hanyar banka masa wuta har ya kone kurmus.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a bayan da jami’an NDLEA suka biyo wata motar da ake zargin tana dauke da masu safarar miyagun kwayoyi. A sakamakon haka, motar ‘yan kwayar ta banke wasu mutane hudu, inda suka rasa rayukansu nan take.

APC Ta Lashe Dukkan Kujerun Shugabancin Kananan Hukumomi Da Kansiloli A Katsina

Wannan lamari ya harzuka jama’ar da ke wajen inda hatsarin ya faru. Marigayi Aliyu Imran, wanda yana daga cikin jami’an da suka bi motar, ya fito daga motarsu domin baiwa jama’a hakuri da bayyana dalilin da ya sa suka biyo motar da gudu.

Sai dai jama’ar da ke cikin fushi ba su saurare shi ba, inda suka far masa da duka, har wani daga cikinsu ya caka masa wuka a ciki.

Wani da lamarin ya faru a gaban idonsa ya shaidawa manema labarai cewa, maimakon abokan aikinsa su taimaka masa, sun tsere ganin cewa jama’ar sun fi karfinsu. Daga bisani, wani dan sanda da ke kusa da wurin ya dauki Aliyu Imran a babur domin kai shi asibiti. Duk da haka, fusatattun mutanen sun bisu har asibitin, suka fito da shi tare da banka masa wuta har sai da ya kone kurmus.

Advertisement

Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa marigayi Aliyu Imran ya yi aure ne a watan Disamba da ya gabata, kuma matarsa ta yanke jiki ta suma bayan da aka kawo gawarsa domin yi masa sutura.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending