Connect with us

News

Ma’aikatan KSIP Sun Koka Kan Rashin Biyan Su Mafi Karancin Albashi Na N71,000 A Kano

Published

on

Ma'aikatan KSIP Na Koka Kan Rashin Biyan Su Mafi Karancin Albashi na N71,000 a Kano

 

DAGA MUHAMMAD SANI UBA, KANO

Advertisement

Ma’aikatan Kamfanin Zuba Jari da Kadarorin Jihar Kano (KSIP) sun koka kan rashin biyan su mafi karancin albashin naira dubu saba’in da daya (N71,000) da Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta amince da shi tun cikin watan Nuwamba, 2024.

Tun a wancan lokaci ne Gwamnan ya sanar da fara biyan sabon albashin ga dukkan ma’aikatan jihar, amma binciken da jaridar Indaranka ta gudanar ya nuna cewa har yanzu ma’aikatan KSIP ba su ci gajiyar wannan kari ba, duk da cewa tsawon watanni hudu kenan da fara aiwatar da tsarin.

Advertisement

Ma’aikatan Hukumar Samar Da Ruwan Sha Sun Janye Yajin Aiki A Kano

Lamarin na kara tayar da hankalin ma’aikatan, musamman sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ke ci gaba da barazana ga rayuwar talaka.

Bincike ya gano cewa wannan jinkiri na biyan albashi ya yi kama da irin wanda ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kano (Water Board) suka fuskanta a watannin baya, lamarin da ya kai su ga tafiya yajin aiki domin neman hakkinsu.

Advertisement

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Kano ta dakatar da Mai Rikon Mukamin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati bisa zargin take ka’idojin albashi, lamarin da ya nuna kokarin gwamnati na gyara tsarin albashi a jihar.

A halin yanzu, ma’aikatan KSIP na ci gaba da zuba ido domin ganin Gwamnatin Kano ta sa baki wajen tabbatar da aiwatar da sabon tsarin albashin kamar yadda aka alkawarta.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending