Connect with us

News

Ana Zargin Jami’an SUBEB 6 Da Karkatar Da Naira Miliyan 96

Published

on

SUBEB

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta  (EFCC) reshen Ilorin ta gurfanar da wasu jami’an Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Kwara (SUBEB) a gaban kotu. Ana tuhumar waɗannan jami’an da aikata laifuka huɗu na cin amana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati, wanda ake cewa sun kai naira miliyan 96.

Advertisement

A cewar sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na EFCC, Dele Oyewale ya fitar, jami’an da ake tuhuma sun haɗa da:

Kungiyar Ƴan Jarida Masu Daukar Hoto da Bidiyo Ta Kano Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Ma’aikacin Daily Nigerian

Ahmed Husain Olarewaju – Daraktan Kuɗi da Kayayyaki

Advertisement

Omole Omololu John – Mai Kula da Lissafin Kuɗi

Fatai Oyerinde – Ko’odinatan Sashen Albashi

Advertisement

Mujeeb Ibrahim – Jami’in Lissafi

Salami Temitope Bashir da Dauda Aweda Quozim – Ma’aikatan Sashen Albashi

Advertisement

Ana zargin cewa tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020, waɗannan jami’an (SUBEB) sun haɗa baki wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar zuwa aljihunsu, inda suka raba a tsakaninsu.

Bayan karanta tuhumar, dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta aikata laifin. Lauyan EFCC, Andrew Akoja, ya nemi a sanya ranar fara shari’a tare da tsare su a gidan gyaran hali, yayin da lauyansu, Abdullahi Lawal, ya nemi a ba su beli.

Advertisement

Alƙalin kotu, Mai Shari’a Akanbi, ya ɗage shari’ar zuwa ranar Laraba, 16 ga Afrilu, 2025 domin ci gaba da sauraron ƙarar, kuma ya bada umarnin a tsare waɗanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na Ilorin har zuwa lokacin shari’a.

Wannan lamari na ƙara jaddada muhimmancin yaki da cin hanci da rashawa, musamman a fannonin ilimi inda kuɗaɗen gwamnati ke taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsarin ilimi a jihohi.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending