News
Kungiyar Ƴan Jarida Masu Daukar Hoto da Bidiyo Ta Kano Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Ma’aikacin Daily Nigerian
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar ƴan jarida masu daukar hoto da bidiyo ta Kano ta bayyana alhini da kunci kan rasuwar Abdullahi Ibrahim, ma’aikacin gidan jaridar Daily Nigerian, wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota a jihar Kano.
Sanarwar da kungiyar ta fitar a yau Laraba ta bayyana marigayin a matsayin kwararren dan jarida, mai kwazo da jajircewa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen daukar labarai da suka ilmantar, fadakar da kuma wayar da kan al’umma.
AJ Supplies Bread: Burodi Mai Dadi, Inganci da Saukin Farashi!
“Abdullahi Ibrahim mutum ne da kwarewarsa da kirkirarsa suka ba shi matsayi na musamman a fagen aikin jarida. Kyamararsa ba kawai tana daukar hotuna ba, tana ba da labaru masu gamsarwa da suka ba marasa magana murya tare da haska batutuwa masu muhimmanci.”
Kungiyar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da duka ƴan uwa da abokan arziki, tare da addu’ar Allah ya gafarta masa, ya ba shi hutawa a Aljannar Firdausi, ya kuma ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu a jiya Talata sakamakon bige shi da wata mata ta yi da mota a kan hanyarsa ta zuwa ofis, inda ya rasu ya bar mata da ƴaƴa uku.
Allah ya jikansa
da rahama.
