Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Fi Kowa Hantarar Yan Jarida A Shekarar 2024 — Bincike

Published

on

Jami’an Tsaro Sun Fi Kowa Hantarar Yan Jarida

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar kare hakkin yada labarai (MRA) ta bayyana cewa hukumomin tsaron Najeriya sun fi kowa kaiwa yan jarida hari a shekarar 2024 a fadin Najeriya.

Advertisement

A cikin wani rahoto da aka yiwa lakabi da “‘Yancin Kafofin yada labarai na fuskantar barazana: Yancin Kafafen Yada Labarai da Tsaron ‘Yan Jarida a Najeriya 2024,” MRA ta bayyana cewa hukumomin tsaro sun kasance kamar Annabi da kafiri da su da yan jarida a fadin Najeriya.

DA DUMI-DUMI: Gobara Ta Tashi A Gidan Man NNPC A Kano

A cewar rahoton, cikin hare-hare 64 da aka kai wa ‘yan jarida a shekarar 2022, 29 hukumomin tsaro ne suka kai su, wanda ke wakiltar kusan kashi 45% na harin da ake kai. Adadin da ya karu zuwa 34 daga cikin hare-hare 77 da aka kai a shekarar 2023, wanda ke wakiltar kusan kashi 44%. Sai dai, lamarin ya sake kamari a shekarar 2024, inda hukumomin tsaro ke da alhakin kai hare-hare 45 cikin 69 kan ‘yan jarida, wanda hakan ke da kashi 65%.

Advertisement

Haka kuma bayanai sun nuna laifuka 21 na cin zarafi cikin watanni 10 na farkon shekara; kesa kesai 17 kan tsare yan jarida ba bisa ka’ida ba shari’o’i uku na kai farmaki a gidaje da ofisoshin ‘yan jarida;Barazana ga rayuwar su; shari’o’i biyu na cin zarafi, sace su, Da kuma hana yan jarida gudanar da ayyukansu har sau biyar; Sannan kuma An kashe dan jarida daya da kuma wasu nau’ikan hare-hare guda shida.

Jami’in tsare-tsare na MRA, Mista John Gbadamosi, a cikin wata sanarwa da ya sanar yayin kaddamar da rahoton, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da hantarar ‘yan jarida, inda yake mai cewa “cibiyoyin da aka dora wa alhakin tabbatar da doka da oda a kasa akwai yan jarida, su ne kam gaba amma kuma sai gashi suma abin hantara ”.

Advertisement

Mista Gbadamosi ya kara da cewa “Abin da ya fi muni shi ne yadda al’adar rashin hukunta masu laifi ke kara yaduwa wanda ya tabbatar da rashin daukar mataki kan hare-haren da aka kai a baya wanda hakan ya karfafa gwiwar wadannan masu aikata ta’addanci wanda a yanzu muke ganin bakin su.”

A karshe MRA ta yi kira da a dauki matakan gaggawa don ganin an kare ‘yan jarida tare da hukunta masu kai musu hari. Hakan ya hada da karfafa tsarin shari’ar Najeriya don kare yan‘yan jaridu da kuma tabbatar da cewa an gaggauta binciken duk wani harin da ake kai wa ‘yan jarida tare da hukunta masu laifi nan take.

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending