News
An Kullewa Gwamna Fubara shiga Kofar Majalisar Dokokin Ribas
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta hana Gwamna Similanayi Fubara shiga cikinta a safiyar wannan Larabar.
Aminiya ta rawaito gwamnan ya ziyarci majalisar da ke yankin Aba na birnin Fatakwal ne domin gabatar mata da Kasafin Kuɗin jihar na 2025.
Sai dai isowar gwamnan tare da tawagarsa, ya tarar da ƙofar shiga majalisar a garƙame da kwaɗo kuma an ƙi buɗewa da ke tabbatar da alamar ba a maraba da zuwan nashi.
Babu wani ƙwaƙwaran dalili da aka bayar, sai dai bayanai sun rawaito cewa an rufe wa gwamnan ƙofa ne saboda bai sanar da majalisar a hukumance cewa zai zo gabatar da Kasafin Kuɗin jihar ba.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
