Connect with us

News

Lauya Ya Maka Alƙali A Babbar Kotun Tarayya Bisa Zargin Cin Zarafi

Published

on

Kotu

 

A wani lamari da ba kasafai ake samu ba, wani lauya mai zaman kansa, Barista Isa Hassan Na Laraba, ya maka wani alƙali a gaban Babbar Kotun Tarayya bisa zargin cin zarafi.

Advertisements
Advertisements

Babbar Kotun Tarayya da ke Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Justine Olajunwon, ta fara sauraron karar da Barista Isa Hassan Na Laraba ya shigar. Lauyan ya shigar da ƙara ne kan Mai Shari’a Abdullahi Hassan Shams Shama, wanda ke shari’a a Babbar Kotun Doma, yana zarginsa da cin zarafi.

Advertisements

Wannan shari’a ta ja hankalin al’umma, kasancewar ba kasafai ake samun irin wannan ƙara daga lauya zuwa alƙali ba. Ana sa ran shari’ar za ta ci gaba da gudana yayin da kotu ke tantance hujjoji daga ɓangarorin da suka shigar da ƙara da kuma waɗanda ake ƙara.

Advertisements
Advertisements

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending