Connect with us

News

Mata Da Ke Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga Ta Shiga Komar ‘Yan Sanda

Published

on

 

Rundunar ‘yan sanda ta kama wata mata mai suna Hauwa Sani da ake zargi da safarar makamai zuwa hannun ‘yan bindiga a Jihar Katsina.

Advertisement

Bincike ya nuna cewa ta boye harsasai 124 a cikin jarka mai ɗauke da manja don kaucewa jami’an tsaro. An cafke ta ne a kan titin Keffi zuwa Abuja ta hannun Rundunar Musamman ta ‘Yan Sanda (Special Tactical Squad).

GOMAN KARSHEN RAMADAN: Dama Ta Ƙarshe Ga Mai Neman Rahamar Allah

Mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa Sani ta amsa laifinta, inda ta ce wani mutum mai suna Nasiru daga Daura ne ya umarce ta da kai wannan makamai.

Advertisement

Rundunar ‘yan sanda ta yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da abubuwan da ka iya zama barazana ga tsaro tare da bayar da rahoto ga hukumomin da suka dace.

 

Advertisement

 

WIKKI TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending