News
NAPTIP ta tseratar da yara 35 da za ai safarar su zuwa nahiyar turai
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Hukumar Yaƙi da Safarar Ɗan’adam, NAPTIP ta tseratar da yara 35 da za a yi safarar su zuwa nahiyar Turai a Ƙasar Nijar.
Shugaban Shiyyar Kano na hukumar, Abdullahi Babale shi ne ya baiyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a jiya Juma’a.
Ya ce an miƙa waɗanda a ka tseratar ɗin ga jami’an Hukumar kula da Shige da Fice ta Ƙasa, inda su kuma su ka miƙa su ga Hukumar NAPTIP a bodar Kongolam da ke Maiadua a Jihar Katsina.
Ya ce waɗanda a ka tseratar ɗin sun haɗa da maza 6 da mata 29 kuma ƴan shekaru 6 ne zuwa 42 da a ka yi safarar su da ga jihohin Ondo, Lagos, Enugu, Anambra, Oyo, Imo, Ogun, Ekiti, Edo, Osun, Kogi da Abia.
“Za a tafi da su zuwa nahiyar Turai ne ta bodar Nijar kuma mun fara bincike a kan lamarin,” in ji Babale
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
