News
YANZU-YANZU: Muaz Magaji ya fice da ga APC
Daga maryam bashir musa
Fitaccen ɗan adawar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Muaz Magaji, ya fice da ga jam’iya mai mulki ta APC a Jihar Kano.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa Magaji na fuskantar Shari’a da Ganduje a kan laifin ƙage da yarfe a kan gwamnan, lamarin da ya sanya ya shafe kusan makonni biyu a gidan yari, kafin da ga bisani a bada belin shi.
A yau Asabar Magaji, wanda a ka fi sani da Ɗan-Sarauniya ya sanar da ficewar ta sa da ga APC a wani taƙaitaccen sako da ya wallafa a sahfinsa na facebook.
Ɗan-Sarauniya, wanda shi ne tsohon Kwamishinan Aiyuka da Gine-gine na Jihar Kano, ya ce al’umma su shaida cewa ya bar APC.
Ƙarin bayani na nan taf…..
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
