News
Nan da Wata Shida Za a Kammala Ginin Majalisar Dokokin Jihar Rivers – Ibas
Shugaban gwamnatin riƙon-ƙwarya na Jihar Rivers, Ibok Ibas, ya bayyana cewa cikin wata shida za a kammala sake gina ginin majalisar dokokin jihar.
Ibas ya bayyana haka ne a yayin ziyarar gani da ido da ya kai a harabar majalisar a ranar Asabar. Ya ce ya lura da muhimmancin kammala aikin cikin lokaci domin tabbatar da cewa majalisar na da ingantaccen wurin gudanar da ayyukanta.
Kwastam Sun Kama Dala 193,000 Da Aka Ɓoye Cikin Kwalayen Yoghurt
Ya buƙaci ɗan kwangilar da ke aikin da ya ƙara gaggauta kammala ginin kamar yadda yarjejeniyar kwangilar ta tanada, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Ibas, aikin sake gina majalisar na daga cikin matakan da gwamnatin ke ɗauka domin tabbatar da cewa bangaren majalisa ya samu cikakken ƙarfi don gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
“Na ga yadda ɓangaren zartarwa yake, yanzu abin da ake buƙata shi ne inganta bangaren majalisa. Kuma ba za su yi aiki cikin natsuwa ba, sai sun samu wurin aiki mai kyau,” in ji Ibas, wanda ya samu rakiyar Shugaban Ma’aikatan Jihar, Dokta George Nwaeke.
