News
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin da Talata a Matsayin Ranar Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah Ƙarama
Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Magdalene Ajani, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, ta fitar a ranar Laraba.
Haɗin Gwiwa Tsakanin Gwamnati Da ‘Yan Jarida Shine Mafi Dacewa Don Ci gaban kano —Aminu Bala
Ministan ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira ga su rungumi dabi’un hakuri, tausayi, kyauta, da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i don zaman lafiya, daidaito, da ci gaban kasa.
Tunji-Ojo ya yi fatan cewa wannan biki na Sallah Ƙarama zai kara hadin kai da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban a kasar.
A karshe, ya bukaci jama’a da su yi bukukuwa cikin lumana da kiyaye doka, tare da tunawa da marasa galihu ta hanyar ayyukan alheri .
Gwamnati ta kuma aika da fatan alheri na Eid Mubarak ga daukacin al’ummar Musulmi, tana mai addu’ar Allah Ya kawo albarka, nasara.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
