Connect with us

News

An kwace kusan rabin zinaren Rasha da kudadenta na kasashen waje

Published

on

Advertisements
ads

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Advertisements
Advertisements

Rasha ta ce tana jiran taimakon China domin shawo kan matsalar tattalin arziki da take fuskanta sakamakon takunkumin da kasashen yamma suka sa mata.

A ranar Lahadi ne Rasha ta ce an kwace kimanin rabin zinarenta da kudaden ajiyarta na waje.

Ministan harkokin wajen Rasha Entov Siluanov ya ce, “Muna da wasu zinaren mai yawa da kuma kdaden kasar wajen a kudin China na Yuan. Kuma muna jiran ganin yadda kasashen yamma za su sanya masu matsin lamba kan harkokin kasuwanci. Babban abin da za su yi shi ne kwace kadarorinmu.”

“Amma na yi amannar sakamakon alakarmu da China, za mu ci gaba da lallaba abin da yake hannunmu,” in ji shi. Ba wai kawai lallabawa ba, za mu ci gaba da kasuwanci a inda kasuwancin yamma ya yi kasa.

Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending