News
Allah Ya Yiwa Galadiman Kano Alh Abbas Sunusi Bayero Rasuwa.
Allah ya yi wa Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi rasuwa yana da shekara 92 a duniya, bayan ya sha fama da jinya. Alhaji Abbas Sanusi shi ne yake riƙe da sarauta mafi girma bayan sarki a tsarin masarautar Kano.
Wata sanarwa da ta fito daga cikin iyalansa ta tabbatar da rasuwar, inda ta ce nan gaba za a bayyana lokacin da za a yi masa jana’iza.
Allah Ya Yiwa Galadiman Kano Alh Abbas Sunusi Bayero Rasuwa.
Alhaji Abbas Sunusi kawu ne ga Sarki Muhammadu Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas.
Shi ne basarake mafi daɗewa a Masarautar Kano. Mahaifinsa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ɗaya ne ya fara naɗa shi sarauta a 1959.
Ya riƙe sarautu da dama da suka haɗa da Sarkin Dawakin Tsakari Gida, da Ɗan Iya, da Wambai da kuma Galadima. Tun zamanin Sarkin Kano Ado Bayero yake riƙe da matsayin Babban Ɗan Majalisar Sarki.
