Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Na’urorin Sola Zuwa Najeriya.

Published

on

solar electricity (1)

Cibiyar bunkasa harkokin masana’antu masu zaman kansu a Najeriya ta nuna matukar damuwa kan sabon shirin da gwamnatin tarayya ke kokarin aiwatarwa na dakatar da shigo da na’urorin samar da hasken rana (solar) daga kasashen waje.

Cibiyar ta bayyana cewa wannan matakin zai kara tsananta matsalar wutar lantarki da ke addabar al’ummar kasar.

Advertisement

‘Yan Sanda Sun Gayyaci Sarki Sunusi Kan Rikicin Da Aka Samu A Tawagarsa A Ranar Sallah

Shugaban cibiyar, Dr Muda Yusuf, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce Najeriya na fuskantar matsananciyar matsala ta rashin wutar lantarki, kuma yanzu da dama daga cikin ‘yan kasa da masana’antu na dogaro da na’urorin sola a matsayin madadin wutar lantarki.

“Yanzu ba lokacin da ya dace ba ne a dakatar da shigo da kayayyakin sola,” in ji Dr Yusuf. “Wannan matakin zai kara jefa miliyoyin mutane cikin duhu da matsin rayuwa, musamman a lokutan da tattalin arziki ke fuskantar kalubale.”

Advertisement

Wannan martani na Dr Yusuf ya biyo bayan sanarwar Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, wanda ya bayyana cewa gwamnati na shirin hana shigo da na’urorin sola domin karfafa masana’antun cikin gida. Sai dai Dr Yusuf ya jaddada cewa Najeriya ba ta da isassun masana’antun da za su iya samar da wadannan na’urori cikin gaggawa da kuma inganci da zai biya bukatun kasa.

“Wannan ba karfafa masana’antu ba ne, illa dai kara dagula rayuwar jama’a da ke kokarin fita daga kangin rashin wuta,” in ji shi.

Advertisement

Cibiyar ta bukaci gwamnati da ta sake duba wannan shawara, tare da samar da tsarin da zai bai wa masana’antun cikin gida tallafi da goyon baya ba tare da hana shigo da kayan da ke taimaka wa rayuwar al’umma kai tsaye ba.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending