News
Gwamnoni Sun Hana Shugabannin Kananan Hukumomi Buɗe Asusu A CBN
A yayin da kotun ƙoli ta bada umarni na buɗe asusun ajiya a Babban Bankin Najeriya (CBN) domin ganin kuɗaɗen ƙananan hukumomi na shigowa kai tsaye daga gwamnatin tarayya, wasu gwamnoni na ƙasar sun fara amfani da karfi da barazana wajen hana shugabannin ƙananan hukumomi aiwatar da wannan doka.
Wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin da suka tattauna da Jaridar PUNCH sun bayyana cewa gwamnoninsu sun ja musu kunnen tare da yi musu barazana da hukunci idan har suka yi yunƙurin buɗe asusun.
Wani shugaban ƙaramar hukuma daga yankin Kudu Maso Gabas ya ce gwamnan su ya ƙi amincewa da maida rabon kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen da suke samu a kowane wata, duk da sun nuna shirinsu na bashi wannan kaso domin su samu damar buɗe asusun kamar yadda gwamnati ta bukata.
Amnesty International Ta Yi Allah-wadai Da Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Najeriya
A gefe guda kuwa, shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi a Jihar Nasarawa, Adamu Sharhabilu, ya tabbatar da cewa ƙananan hukumomin jihar sun riga sun buɗe asusun, suna kuma dakon karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga gwamnatin tarayya.
Wannan lamari ya sake jaddada rikicin tsakanin gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi a kan ikon mallakar kuɗin da suka dace da su, inda ake ganin yana da nasaba da yunkurin gwamnati na tabbatar da cikakken ‘yancin cin gashin kansu.
