Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Janye Jerin Sunayen Wadanda Ya Nada Bayan Lura da Kurakurai  

Published

on

Shugaba Tinubu ya bayyana makomar TETFUND da NITDA da NASENI

 

Fadar Shugaban Ƙasa ta Najeriya ta janye jerin sunayen sabbin nadin da aka fitar a ranar Juma’a, bayan da aka gano cewa akwai kura-kurai a cikin jerin.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani sako da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Sunday Dare, ya wallafa a shafin sa na X

A cewar Dare, jerin sunayen da aka fitar sun haɗa da mutane 152 daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da wakilai daga yankin Arewa maso Yamma – yankin da ke fuskantar matsanancin rashin tsaro – da kuma mutane 29 daga Kudu maso Yamma.

Shugaba Tinubu Ya Janye Sunayen Sabbin Nadi Bayan Lura da Kurakurai  

Sai dai duk da cewa an bayyana cewa an tafka kurakurai a cikin jerin, rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa ya nuna cewa jerin sunayen bai rasa sunayen muhimman mutane ba, ciki har da na shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Yankin Kudu maso Gabas kuwa ya samu mutane 16 a cikin jerin, wanda ke nuna karancin wakilci idan aka kwatanta da wasu yankuna.

Advertisement

Ko da yake ba a bayyana takamaiman kurakuran da aka yi ba, ba kuma a fayyace dalilin janye jerin ba, wasu na ganin wannan mataki yana da nasaba da zarge-zargen nuna son kai da rashin daidaito da ake wa Shugaba Bola Tinubu tun bayan darewarsa kan karagar mulki a watan Mayu na shekarar 2023.

Yan Najeriya da dama sun dade suna bayyana damuwa kan yadda nadin manyan mukamai ke fifita yankin Kudu maso Yamma – inda Shugaba Tinubu ya fito – fiye da sauran yankuna na ƙasar.

 

 

 

FRI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending