News
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Abba Kyari Da Wasu Jami’ai Da Ake Zargi.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci mai muhimmanci a shari’ar da ta shafi tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari, da wasu jami’an ‘yan sanda guda hudu, wadanda ake tuhuma da laifin mu’amala da miyagun kwayoyi.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya jagoranci zaman kotun, inda ya bayyana cewa akwai hujjoji masu karfi da ke bukatar wadanda ake tuhuma su gabatar da kariya ga kansu, bayan kotu ta yi watsi da bukatarsu ta a wanke su ba tare da sun kare kansu ba (no-case submission).
‘Yan Majalisar Arewa Maso Gabas Sun Zargi Gwamnatin Shugaba Tinubu Da Wariya
Tare da Abba Kyari, wadanda ke fuskantar shari’ar sun hada da: ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insp. Simon Agirgba, da Insp. John Nuhu. Ana zarginsu da hada baki wajen mu’amala da kwayoyi masu nauyin kilogiram 17.55, da kuma yunkurin lalata shaidar wata kwaya mai nauyin kilogiram 21.35.
Alkalin kotun ya jaddada cewa ko da adadin kwayar da ake tuhuma ya ragu, hakan ba zai kawar da hujjojin da ke bukatar wadanda ake zargi su kare kansu a gaban kotu ba.
Tun bayan kama su a shekarar 2022, wadanda ake tuhuma sun ci gaba da musanta aikata laifin. A gefe guda kuma, wasu daga cikin wadanda aka kama tare da su – Chibunna Umeibe da Emeka Ezenwanne – sun amsa laifi, kuma an yanke musu hukunci.
Kotun ta dage cigaban sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga Mayu, domin wadanda ake tuhuma su fara kare kansu kan zarge-zargen da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ke musu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
