News
Tsohon Maitaimakin Gwamna a Adamawa ya fice daga APC zuwa NNPP
Daga Khadija Ibrahim Muhammad
Tsohon Mataimakin Gwamna a Jihar Adamawa, Sa’ad Tahir, ya fice da ga Jami’yar APC zuwa NNPP.
Tahir ya sanar da sauya shekar ta sa ne a wani taron manema labarai a Yola a yau Talata.
A tuna Tahir ya zama Mataimakin Gwamna ne ga Bala Ngilari a 2014 a jam’iyar PDP, lokacin da a ka naɗa shi a matsayin mataimaki bayan da kotu ta kori Ahmadu Fintiri, lokacin yana gwamna na riƙon ƙwarya, sai shi Ngilari, lokacin yana Mataimakin Murtala Nyako da a ka tsige, ya zama gwamnan.
A 2018, sai Tahir ya fice da ga PDP zuwa APC inda ya kasance a cikin har zuwa yau da ya sanar da ficewar sa da ga cikin jam’iyar.
Ya ce daya da ga cikin dalilan da su ka sanya ya ɗau wannan matakin shine domin ya kare martabar dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
-
News4 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News2 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News2 days ago
Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha
