News
A taron da shugabannin jam’iyyar PDP suka yi a Abuja.
Daga yasir sani abdullahi
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya baiyyana cewa.
Duk jam’iyyar da ta rasa mutum ko da daya ne, to wajibi ne ta nuna damuwar ta.
Yace amma duk mutumin da yake yi mata zagon kasa dole ta ji dadi idan ya fita.
Don haka su a jam’iyyar PDP suna murna da fitar duk wanda yayi musu zagon kasa musamman a zaben 2019an da ya wuce.
Atiku yace PDP jam’iyyar kowa ce ba ta wani mutum ba.
Wadan da suka kafa ta basu damka ta a hannun kowa ba ballantana yace ta sa ce.
Yace akwai mutanen kirki da yawa wadan da suke son shigowa cikin ta.
Amma sun ki shiga saboda ganin masu yi mata zqgon kasa a cikin ta.
Daga karshe Atiku ya roki ALLAH SWT yasa fitar su ta zama alkhairi ga Najeriya baki daya.
-
News4 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News2 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News2 days ago
Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha
