News
Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Jita-Jitar Sauke Ministocin Tsaron Najeriya
Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke ministocin tsaron Najeriya da ministan lantarki.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa labarin da aka fitar da shi ta kafar Phoenix Browser labari ne na bogi kuma karya ce tsagwaronta. Ya kara da cewa, “Wadanda ke yada irin wannan labari na bogi, masu laifi ne da ya kamata a hukunta su ba tare da bata lokaci ba.”
NUJ Ta Bukaci Kwamishinan Lafiya Ya Ƙarfafa Yaƙi Da Cutar Zazzabin Cizon Sauro A Kano
Phoenix Browser ta fitar da labarin da ke cewa an sallami ministocin tsaro da ministan lantarki, amma fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa babu wani sauyi a jerin ministocin da ke kan mukami a yanzu.
Bayo Onanuga ya bukaci jama’a da su daina yarda da jita-jita marasa tushe tare da kiran hukumomi da su dauki mataki kan wadanda ke yada irin wannan labari don tayar da hankali a cikin al’umma.
