News
Gwamnatin Tarayya Ta Aiyana Ranar 1 Ga Watan Mayu A Matsayin Ranar Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu domin bai wa ma’aikata damar gudanar da bikin ranar ma’aikata ta bana.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ranar 1 ga watan Mayu za ta zama ranar hutu a wannan shekara, domin bai wa ma’aikatan Najeriya damar gudanar da bikin ranar ma’aikata na bana, wanda ake gudanarwa a kowacce shekara.
Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Jita-Jitar Sauke Ministocin Tsaron Najeriya
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Talata. A cikin sanarwar, Tunji-Ojo ya nuna yabon sa ga ma’aikatan Najeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi wajen ganin kasar ta samu cigaban da ake fata.
Ministan ya kuma kara da cewa, yana da muhimmanci ma’aikatan kasar su ci gaba da nuna kirkira da ingantaccen aiki, domin ci gaban tattalin arzikin Najeriya da kuma inganta rayuwar al’umma baki daya.
